ProZ.com translation contests »
32nd Translation Contest: "Movie night" » English to Hausa » Entry by Nafisat Lawal


Source text in English

Translation by Nafisat Lawal (#36665) — Winner

To say that I was compelled by Parasite from start to finish is an understatement; its filming style with tracking shots are enthralling. Having watched several Korean films during the London Korean Film Festival, I was familiar with the usual genres employed in such films but Parasite seemed to defy them all! Parasite is comedic, in a quirky way, it is also a thriller, straddles class divisions and also depicts a family tale amongst other genres and is therefore likely to appeal to all ages.

Parasite truly deserves to be watched in a cinema to appreciate its nuances and the stylish cinematography. As a summary, to avoid spoilers, Parasite tells the tale of the interaction between the Park family and the Kim’s, an unemployed family, whose contrasting worlds collide with long lasting consequences.

[...]Bong Joon-Ho manages to pique the audience’s interest with brightly lit shots coupled with the effective use of indoor space, and it is surprising to realise, after the film’s 2 hour 12 minute length, that most of the scenes occur within the Park family’s home. The mundane elements of domesticity are displayed with an intriguing perspective showcasing Bong Joon-Ho’s flair. It is a slow burner but you will revel in its beauty and ingenuity as Parasite convinces that it operates solely on one level but it is in fact multi-layered and depicts social realism with empathy and pathos.

The cast are beguiling to watch, every facial movement and action is accentuated, even the mere act of walking up or down stairs can convey hidden meaning, which the camera fragments. Levels of unease are also created by virtue of that effective use of space with unusual camera angles and dramatic weather conditions ratcheting up that sensation. There is a surreal nature to Parasite, which its score emphasises, and furthermore the film adopts elements of the absurd devised in such an ingenious way which is truly cinematic magic. Parasite’s apparent eeriness will certainly keep you riveted and would not feel alien to the Twilight Zone school of filmmaking.

The actors are very impressive and add breadth to their roles creating relatability whilst seeming effortlessly cool. When Ki-Woo and Ki-Jeong Kim were working within the Park family home as private tutors they certainly epitomised this level of nonchalant, understated authority creating an aura of mysticism with the unspoken, almost mythical, tutoring techniques employed. Quite simply, the actors Park So-Dam and Choi Woo-Sik, as Ki-Woo and Ki-Jeong, are compelling to watch in the different directions that Parasite follows and they carry these performances seamlessly thereby inviting the audience to be on their side.

[...]Parasite is a remarkable piece of extremely skilful filmmaking, it is simply a must see film, and so I am looking forward to re-watching the film on its UK general release date.
Irin daukar hankali na da Parasite yayi tun daga farko har zuwa karshe ba zai misaltu ba; Salo da bin diddigi na fim din abun ban sha'awa ne. Bayan kallon fina-finan Koriya da yawa da na yi a lokacin bikin fina-finai na Koriya a London, na saba da nau'ikan da aka saba amfani da su a cikin irin waɗannan fina-finai amma Parasite ya fi su duka! Parasite yana da ban dariya na musamman, laifi da kisan kai, yana nuna rabe-raben aji na mutane, kuma yana nuna labarin dangi tare da sauran nau'ika saboda haka ya na iya jan hankalin yara da manya gaba daya.

Gaskiya Parasite ya cancanci a kalle shi a gidan kallo domin godewa inuwar sa da kuma salon hada fim din. A takaice dai, don kada na baku satar amsa da yawa, Parasite yana bada labarin cudanya ne tsakanin dangin Park da dangin Kim, dangin da ba su da aikin yi, waɗanda banbancin duniyar su ya yi karo da mummunan sakamako mai dorewa.

[...]Bong Joon-Ho yayi kokari gurin daukar hakalin masu kallo da hotuna masu haske tare da ingantaccen amfani da sararin cikin gida. Abin mamakin shine, bayan tsahon sa'o'i 2 da mintuna 12, wanda yawanci al'amura suna faruwa ne a cikin gidan dangin Park. An baje kolin abubuwan da suka shafi cikin gida tare da hangen nesa mai ban sha'awa wanda ke nuna hazaƙar Bong Joon-Ho. Yana da jinkirin daukar hakali amma za ku yi murna da kyau da basirar sa saboda Parasite ya tabbatar da cewa yana aiki a mataki daya ne amma a zahiri yana da nau'i-nau'i da yawa kuma yana nuna gaskiyar zamantakewa gami da tausayi da cutarwa.

Yan fim din suna da jan hankali, sun jaddada ko wanne motsin fuska da kuma aiki, kai hatta hawa bene da sauka yana isar da boyayyiyar manufa, wanda kyamara ta gutsuttsura. Har ila yau, an kirkiri matakan rashin jin daɗi ta hanyar ingantaccen amfani da sararin samaniya tare da kusurwoyin kyamara da ba a saba gani ba da yanayin yanayi daban daban daya karawa abun armashi. Akwai wani abun ban mamaki a game da Parasite, wanda makin da ya samu ya nuna hakan, budu da kari fim din yana dauke da abubuwan shashanci da aka kirkira cikin fasaha wanda ya gaskata sihirin finafinai. Tabbas bayyanannen ban tsoro na Parasite zai saka ka cikin rudu sannan baza ka zama bako a yankin makarantar yin fim ba.

Yan wasan kwaikwayon suna da matukar ban sha'awa kuma suna kirkirar alaƙa ta hanyar karawa rawar da suke takawa armashi ba tare da nuna kosawa ba. Lokacin da Ki-Woo da Ki-Jeong Kim ke aiki a cikin gidan dangin Park a matsayin masu koyarwa masu zaman kansu, tabbas sun nuna halin ko in kula, iko mara tushe wanda ya bayyana halin su na sufi na boyayyun al'amura, da yin amfani da dabarun koyarwa kusan na almara. Kusan A sauƙaƙe, tilas a kalli yan wasa Park So-Dam da Choi Woo-Sik, wanda suka fito a matsayin Ki-Woo da Ki-Jeong a hanyoyi daban-daban da Parasite ya bi gurin jan hankalin masu kallo, kuma sun ja ra'ayin masu kallon ta hanyar yin aikin su ba tare da wata matsala ba.

[...]Parasite wani yanki ne mai ban mamaki na shirya fina-finai ƙware. Kawai fim ne wanda dole a kalla, don haka ina sa ran sake kallon fim ɗin a ranar fitowar sa ta gabaɗaya a Burtaniya.


Discuss this entry